Wani mai hoto ya yi ramuwar gayya kan abun da kanwar amarya ta yi masa a wajen biki.
Matashiyar wacce ta yi rabon abinci ta hana mai hoton shinkafar biki kuma hakan ya yi masa ciwo.
Don rama abun da ta yi masa, mutumin ya yanke ta daga gaba daya hotunan da ya dauka.