Ticker

6/recent/ticker-posts

ANNOBA: An Fara Sacewa Mutane "Mazakutar" Su A Kano GA yadda yafaru

 


ANNOBA: An Fara Sacewa Mutane "Mazakutar" Su A Kano 


Wata annoba da ta Kunno Kai kwanan nan A Arewacin Najeriya wadda ta faro daga jihohin Zamfara Bauchi Kebbi, ta famtsama zuwa jihohin Arewa sosai.


Jaridar AMINTACCIYA ta jiyo cewa baya ga shanye jinin matan Aure na cikin gida da, mutanen ke yi, suna kuma sacewa mutum gaban sa.


Idan baku manta ba, a kwanan nan mun kawo muku wasu rahotanni yadda mata ke shiga gidajen matan Aure da sunan suna so a basu ruwa ta yadda da zarar mace ta juya sai ta faɗi, ko ta mutu ko ta suma, sau da yawa ana kama masu laifin kuma suna tabbatar da cewa haƙiƙa suna da yawa.


Wani abin da ya ƙara ɗaga hankali baya ga shanye jini da suke yi, sukan iya kwashewa namiji al'aurar sa, in kuma suka so mace zata iya rasa nonon ta.


Abin ya faro ne daga jihohin Zamfara Kebbi da sauran su, tun ana bada labarin al'umma na ƙaryatawa yanzu haka abin ya fantsama jihohi, kada kai mamaki ko sun shigo yankin ku lallai ka kiyaye.


Wasu na ƙaryatawa cewa babu yadda hakan zai taɓa yiwuwa sai dai sun manta da sihiri gaskiya ne, sannan akwai matsafa wannan ma sun sani amma Dukda haka jama'a na ganin wannan labarin ba gaskiya bane, to waɗanda suka yarda hakan zai iya faruwa su kiyaye.


Ko a jiya wata budurwa ta shaidawa Majiyar mu yadda masu wannan taannati suka fito da sabon salo, tace a unguwar su Tukuntawa dake Kano lamarin ya faru, wato dauke gaban namiji.


Tace a ƙofar gidan su, dake unguwar Tukuntawa, kuma lamarin yana gaban yan Sandan Tukuntawa kusa da unguwar geza yanzu haka,  abin da ya faru ne, wani kutum ne yazo wucewa sai kawai suka gaisa da wani yake cewa yana da tambaya dan Allah dan Annabi.


Suna gaisawa gaba ɗaya ya nemi gaban sa ya rasa, mutumin bai nisa ba, aka kama shi, gaban ya dawo kuma ya sake ɓacewa, ya kwanta yana ihu, aka kaisu police na Tukuntawa ya dawo masa kuma ya ƙara ɓacewa.


Ko a jiya an sami labarin rasuwar wata mata itama sanadin neman taimakon, jiya da yamma ne, wata mata ta shiga wani gida a Unguwar Bakinruwa Bunawa, ta nemi zatayi fitsari matar gidan ta bata dama ta shiga, bayan fitowar ta kuwa Matar gidan ta yanke jiki ta fadi nan take ta rasa rayuwarta. Mata ce ga Nasiru Mal. Nuhu kanin Alh. Hafizu Mal. Nuhu dake unguwar.


Kamar yadda kukaji a yau ne akayi Janaizarta da misalin karfe 8 na safe a gidan mijinta dake Bakinruwa Bunawa.


Yanzu dai naima ake a hana taimakon bayin Allah domin dole an jefa tsoro cikin zukatan al'umma sakamakon ɓullowar ɓata gari.


Jama'a sai a kiyaye kuma a kula da kyau, mu tsananta da addu'a sannan mu kula da shige da ficen bakin fuska a gidajen mu, A yiwa Iyali gargadi da kyau kuma a rike addu'a. 


Allah ya kawo mana karshen matsalolin da ke damun mu