shin kin taba yin mafarkin namijin dare ko ta macen dare, da hakan ya canza miki rayuwa?
biyomu kuji wannan takaiccen labarin :
Ni bana mafarki sosai gaba daya a rayuwata amma bayan na balaga kwatsam sai watarana nayi mafarkin wata tazo ta fara jana da wasa tun ina nuna mata bana son haka har ya kai ga na fara rabuwa da ita, nan tarika tabamun wasu sassa na jikina, tun ina ture hannunta har har yakai ga na fara jin cewa tunda yar uwata ce mace bari kawai na rabi da ita, can sai na fara ji kamar tabani da takeyi ya fara tasiri a jikina, nan dai ban damu ba don ni a lokacin ma ina danne dannan waya ne a mafarkin.
bayan na farka sai sai naji duk jikina be bani ba, kuma duk bayan wasu mintuka sai naji na tuna da abinda ya faru dani a mafarki, bayan kwana daya kwana biyu sai wattanan matar ta kara bayyana mun a mafarki, kuma ta fara tabamin jiki, nan kuma naga na kasa hanata, harma naji so nike tana mun abinda takeyi kuma nima na fara tabata kamar yadda take yi mun, bayan yan kwanaki har idan batazo mun cikin mafarki ba idan na tashi sai naji na fara shiga damuwa, to kuma ni koda yaushe sai na rika jin cewa fa lallai abinda mukeyi be dace ba, kuma ma har na fara jin bana sha'awar ɗa namiji kwata-kwata, to sai abin ya fara sani tunani, da dai naji abin ya dameni sosai sai nayi wa babata magana cewa gafa abinda ke faruwa dani a mafarki, tace babu damuwa na rika addu'a kawai idan zan kwanta, bata wani nuna mun cewa wannan wata matsala ce babba ba, wata rana ina garaurayata a social media sai wata ta turomun friend request, wacce sunanta ya kare da (less) banma san me hakan yake nufi ba, to bayan mun zama friends har mun fara chat da ita sai wata rana ta fara yimun maganar batsa har ma da turomun hotunan batsa, ni kuma ina nuna mata hakan ba wata matsala bace har ta bukaci mu hadu tunda ba wani nisa muke ba a tsakaninmu, nan ta fara turo mun kudin mota har na isa gidanta kai tsaye ashe ma bazawara ce, ban sani ba, nan kawai muka fara wasa da ita, sai ta rika turomun kudi ina zuwa inda take har wata ranar ma idan bata turomun ba kudin mamanmu nakan dauka na je gidanta, a haka na kwashe tsawon lokaci ni banyi aure ba ni ba karatu ba ni ba wata gagarumar sana'ace dani ba, kuma bana sha'awan ɗa namiji, girma ya fara kamani, ciwo ya sameni me tsanani da saida na kusa mutuwa, a wannan ciwon ne na tabbatar da nayi babban kuskure, bayan na warke to sai na fara yiwa kaina karatun ta natsu, na nemi wani malamin da ya taimaka mun da addu'oi da nakeyi har na fara samun saukin rage tunanin komawa halin da na kasance a ciki, amma kuma duk in na sami saurayi bayan kwana kadan sai ya daina kulani, anan na kara shiga wata damuwar duk nabi na rame, kuma anata neman mun magani har na samu daga baya na nayi aure, amma kuma bayan auren sai na rika jin cewa mijina baya gamsar dani, kuma sai na rika jin yana bata mun rai, shima sai yake ganin bana kyauta masa, nan dai zama yaki dadi har ya kai ga mun rabu, na dawo gida, kuma na kasa barin halin da nakeyi da wannan mata don har ina gidan miji takanzo har gidana, haka bayan na fita nima nakanje mu hadu.
To wallahi dai abinda yasa nayi share din wannan labarin shine, akwai irina da yawa a social media da suke ɓata yan mata, kuma a yanzu dai haka ni ba wata lafiya ce dani ba, kuma na kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali har a raina, kuma bani da wani tudun dafawa shi yasa nake tunanin kila wasu idan sukaji halin da nake ciki kila su hankalta, don nima din rashin mafadi yasa har na kai ga wannan halin, wallahi da na sami wanda ya fadamun abinda na fada muku dinnan nasan da ban shiga wani hali ba, kuma ina fatan Allah ya shiryemu dagani har kawar tawa, kuma tabbas ynz haka na fara nesantarta kuma na dage da addu'a ba dare ba rana, ina fatan Allah ya gyara mun rayuwata kuma ya yafeni don nayi nadama matuka.
#####_ gargadi
# harkar less babban illace ga al'umma ta kowani shashi akabi kuwa, kuma bincike ya nuna mafi yawan yawan sanadiyyar hakan shedanun aljanu ne ke bibiyan yaranmu, sbd hakan :
1. duk matar da take jin mijinta baya bata sha'awa to ta nemi magani cikin gaggawa.
2. duk yarinyar da ta fara jin sha'awar ƴar uwanta mace to tayi gaggawan neman magani
3. duk matar da take mafarkin da bata gane mishi kuma ya saɓa da normal mafarki to ta nemi magani ko malamai su bata shawarwari.
Allah ya gyara mana Al'umma kuma ya shiryemu baki daya.