Tun jiya nake ta ganin mutane suna fostin din labarin, amma har zuwa yanzu ban samu cikakken bayani akai ba. Wasu na hasashen cewa, tallafin Man Fetur din ne ake son a dawo dashi koda ba duka ba.
Yawan maganganu da korafi da ‘yan kasar suke yi, musamman a kafofin sada zumunta, yana daga cikin dalilan da yasa Gwamnatin ta fara fahimtar halin da al-umma suke ciki. Akwai abubuwa da dama da idan Gwamnati tayi aka yi shiru, shikenan sai ta dauka kamar babu matsala a kasar.
Akwai abubuwan da idan aka yawaita yin magana akansu da korafi su da kansu zasu fahimci hakan babbar matsala ce, kuma sai kaga sun fasa aiwatarwa.
Muna fata da burin ganin man Fetur ya sauko kasa da yadda sabuwar Gwamnati ta same shi, na tabbata zamuji dadi mu warwasa, abubuwa da dama za su sauko da izinin Ubangiji. Allah ya tabbatar mana da hakan.