Za mu soma shari'a da masu yiwa AA Rufa'i Bidiyo
- Danginsa
Dangin A.A Rufa'i da ake ta yada bidiyonsa a
kafafen sada zumunta da sunan nishadi sun ce za
su soma daukar matakin shari'a ga masu yin
hakan.
Yayin ziyarar da suka kawo gidan Rediyon Dala FM
da ke Kano tare da shi sun bayyana rashin lafiyar
da yake fama da ita, da kuma kokarin da suke
wajen nema masa magani.
Dangane da masu son taimaka masa don ya samu
lafiya sun ce kofa a bude take don taimaka masa
maimakon yin yamadidi da shi.
Ga dai tattaunawarsu da Dala FM.