Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Matashi Yayi Tattaki Da Jihar Katsina Zuwa Kano Don Ganawa Da Matashiyar Da Tayi Alkawarin Bawa Duk Wadda Zai Aurenta Miliya 50

 SO GAMÒN JINI: Wani Matashi Ya Fara Tattaki Daga Jihar Katsina Zuwa Kanó Domin Némań Iziniń Ganawa Da Matashiyar Nań Da Ta Yi Alƙawarin Ba Da Kyautar Gida, Mota Da Jarin Miliyan 50 Ga Wanda Ya Ce Ya Na Sonta Da Aure


Rahotannin da mu ke samu yanzu haka na bayyana cewa wani matashi mai suna Babangida Alolo Ƴandoma ya fara tattaki a ƙafa daga Katsina zuwa 


Kano domin ya nemi soyayyar kyakykyawar bubudurwar nań wacce ta yi alƙawarin ba da kyautar gida, mota, da jarin Miliyan 50 ga duk wanda ya ce ya na sonta zai aure ta.

Matashin ya tabbatar da cewa ba neman kuɗi da gida da motar ne za su sa ya je gun matashiyar ba, zai je ne domin bayyana mata soyayyarsa da ya ke yi mata domin Allah idan ta gan shi ya yi mata to ya yarda ko da gobe ne a ɗaura musu aure zai yi komai da kansa.

Yanzu haka dai an ce matashin ya fara tattakin daga Jihar Katsina zai je Kano domin ya gana da kyakykyawar budurwar ya gan ta ta gan shi Ido da Ido idan har ta ga ya yi mata to shi ya yarda zai aure ta domin so da ƙauna kawai.

Mè zakù cè?