Wannan tsohon da ya haura shekara 100 ya bawa baban wannan yarinyar kudi, ya tilastawa baban yarinyar kashe Auranta akan lallai sai ya aure ta.
Sunan yarinyar Hafsatu Sa'adu, suna zaune a garin Rawayyah dake karamar hukumar Bungudu jihar Zamfara, yarinyar bata wuce shekara 20 da kadan ba.
Kafun auran yarinyar na farko, wannan tsohon da a lokacin ya haura shekara 90, ya nemi Auranta a wurin baban yarinyar ita ba ta ma sani ba, bayan anyi Auran sai dattijon ya dinga bawa mahaifinta kudi akan lallai yasa a saki yarinyar shi kuma ya aure ta.
Tsohon ya bawa mahaifinta kudi masu yawa, yaje kotu ya shigar da kara akan lallai a raba Auran 'yar tashi da matashin tare da yin karyar cewa baisan lokacin da aka daurawa 'yar tashi Aure da saurayin ba.
Tsohon yayi amfani da makudan kudaden da yake da su wurin kashe mata Aure, inda ya kashe sama da dubu 650,000 akan shari'ar har alkalin kotun ya kashe Auran, a lokacin tana da yarinya guda, tana kuma dauke da wani ciki.
A yanzu haka shekarar ta 4 tana zaune a gida bata san Matsayin Auranta ba duk da kasancewar tana son tsohon mijin nata. Dukkannin mutanen garin kowa yana tsoron tinkararta yace Mata yana sonta saboda kudin da tsohon yake da su, ita kuma yarinyar bata son tsohon balle ta yadda ta Aure shi.
Mahaifin yarinyar ya gaji da zaman da take yi a gidan yana son ya kara yi mata Aure. Tsohon ya yiwa mahaifin nata barazanar cewa lallai indai sake daura mata aure da wani to zai daure shi kuma duk sai ya biya shi kudaden da ya bashi da wanda ya kashe a wurin shari'ar, wannan dalilin yasa mahaifin ya hakura babu yadda ya iya domin baida hanyar da zai iya biyan kudaden.
Dalilin hakan yasa yarinyar ta taso tun daga garin nasu taje har cikin birnin Gusau takai kara ofishin Human Right, aka kirawo mahaifin nata, da tsohon da sauran mutanen da lamarin ya shafa.
Daga karshe dai yanzu haka Human Right ta dauki alhakin sake daurawa yarinyar Aure da duk wanda take so. Ga duk mai bukatar jin cikakkiyar tattaunawa da yarinyar da iyayan nata, da tsohon zai iya duba shafin jaridar Mai Biredi TV.
Ya kamata mu dinga saka ido sosai akan irin wa 'yan nan matsalolin, tare da taimakon mutanen da suka tsinki kansu a ciki.
Wallahi irin wa 'yan nan zaluncin da wa 'yanda suka fi haka suna cigaba da faruwa a lungu da sakunan karkara. Wani abun idan kaji sai ka dauka a Fim ne ba'a zahiri ba, Allah ya kyauta ya cigaba da bamu ikon yiwa al-ummar da suke karkashinmu adalci.
✍️ Comr Abba Sani Pantami