Matashiyar nan Ruƙayya Muhammad wacce tayi iƙirarin bada kyautar danƙareren gida da Mota tare da jarin naira Miliyan 50 ga duk wanda ya amince zai aure ta ta bayyana cewar ta soke wannan alƙawari da tayi saboda wasu dalilai Ruƙayya ta ce
"Naji ma wasu na cewa a gidan haya muke nida iyaye na da sauran maganganu na raini da ake ta yi a kaina saboda haka na dakatar da wanan alƙawarin sai zuwa nan gaba in duba don in sake fidda matsaya" In ji ta
A ƙarshen makon daya gabata ne dai Ruƙayya Muhammad tayi shelar neman mijin aure wanda tace zata ba shi kyautar Gida, Mota da Naira Miliyan 50 kamar yadda ta bayyana a faifan Bidiyon, a halin yanzu dai tace ta janye wannan magana da tayi
Ga video Nan
👇👇👇👇👇👇

