Fitacciyar ƴar kasuwar nan Hajjiya Laila Ali Othman ta shawarci ƴan uwanta hausawa da su tashi tsaye wajen yin sana'a da ayyukan dogaro da kai, Laila ta ce "Idan ka ɗauki Hausawa 20 aiki to za kaga lalaci da son jiki da ha'inci
Amma idan ka ɗauki yare mutum 5 aikin da za suyi maka Hausawa 20 basu iya yinsa a yini kuma idan ka basu kuɗi su raina amma shi yare ko nawa ka ba shi sai ya duƙa yayi godiya, saboda haka ni yanzu ba zan iya ɗaukar Bahaushe aiki ba don na san ko sati ba zai yiba zai bari kuma ga rainuwa wai albashin dubu 30-50 yayi masa kaɗan amma zai iya turo maka saƙo hada lambar account yana roƙonka Naira dubu 5 sai kace ya baka ajiya
Sai mutum ya zauna kan hanya da ka wuce yace baka da kirki ai ɗan wutane kai saboda haka ina kira ga ƴan uwana Hausawa da su gyara ɗabi'unsu in jita
