Ticker

6/recent/ticker-posts

VIDEO: “Ba nine na fara yin wasa da Sallah ba Musulmai sun riga ni yin Comedy da ita”—Davido


 Fitaccen mawaƙin kudancin Najeriya Davido ya mayar wa da Musulmai martani, biyo bayan sukar da yake sha a kan Bidiyon waƙar da ya ɗora a shafunsa na sada zumunta yana waƙa a kan ginin Masallaci tare da wasu masu yin Sallah


Mawaƙin ya ce "Ban yi tsammanin abin zai tada ƙura haka ba na zata ba wani abin ɓatanci ko cin mutuncin Addinin Musulunci ne ba, saboda ai na daɗe ina ganin Musulman su da kansu suna yin wasa da Sallah yanzu haka 


A kwai Comedy masu tarin yawa a cikin waya ta na aje,  koda za'a kai ni Kotu zan nuna su don su zama hujja a kan cewa ba nine wanda ya fara wasa da Sallah ba suma Musulman suna shirya Comedy ɗin ta" in ji shi kamar yadda ya bayyana a firarsa da kafar watsa labaran Trace a safiyar yau