Ticker

6/recent/ticker-posts

RAƊAƊIN YUNWA DA TSADAR RAYUWA: Manyan dalilai 10 da su ka haddasa masifar tsadar rayuwa ta afka wa Najeriya –


RAƊAƊIN YUNWA DA TSADAR RAYUWA: Manyan dalilai 10 da su ka haddasa masifar tsadar rayuwa ta afka wa Najeriya – GFSI
Ashafa MurnaibyAshafa Murnai July 18, 2023
RAƊAƊIN YUNWA DA TSADAR RAYUWA: Manyan dalilai 10 da su ka haddasa masifar tsadar rayuwa ta afka wa Najeriya – GFSI
Wani bincike ya tabbatar da cewa musabbabin raɗaɗin tsadar rayuwa da ake fama da shi ya samu asali daga talauci, sauyin yanayi, faɗace-faɗace da tashe-tashen hankula, matsalar tsaro, yawan hayayyafa da kuma rashin tsare-tsaren ci gaba.

Akwai kuma rashin tsare-tsaren harkokin noma, asarar da manoma ke yi bayan girbi, rashin wadatattun kuɗaɗen a kasafi da wasu dalilai da dama.

Ga Su Nan Dalla-dalla:

1. Talauci: Sama da mutane miliyan 43.7 suke
fama da talauci a Najeriya.

2. Sauyin yanayi: Wannan kuma ta haɗa da ambaliya, matsalar rashin wadataccen ruwan sama da wasu matsaloli.

3. Faɗace-faɗace da tashe-tashen hankula: Sun haɗa da masu garkuwa da mutane, ta’addanci da faɗace-faɗacen kabilanci.

4. Matsalar Tsaro: Wadda ke hana manoma zuwa gona.

5. Yawan hayayyafa: An kiyasta yawan jama’a a Najeriya ya kai mutum miliyan 220.

6. Rashin tsare-tsaren ci gaba daga gwamnatocin baya.

7. Rashin tsare-tsaren harkokin noma ta yadda babu wani ci gaban zamani da sauki a harkokin noma.

8. Asarar da manoma ke yi bayan girbi: Musamman saboda rashin tsari na adana abinci.

9. Rashin wadatattun kuɗaɗe a kasafin noma.

10. Cire tallafin fetur ya tayar da
raɗaɗin talauci sosai.

Haka kuma GFSI ya fayyace cewa a Najeriya kashi 12.9 na tantagaryar matalautan duniya su ke.

Jadawalin Rashin Ƙoshin da Abinci, GFSI, ya tabbatar da cewa Najeriya ta zo ta 107 a cikin ƙasashe 113 a duniya.

Wato kenan kashi 12.9 masu fama da matsanancin talauci a duniya, to a nan ƙasar su ke, a lissafin 2022.

Lissafin ya tabbatar da mutum miliyan 43.7 a Najeriya ba su da ƙarfin abinci.

Haka Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO ta ce sama da mutum miliyan 25 za su shiga garari da kuma rashin abinci a Najeriya daga watan Yuni zuwa Agusta.