Ticker

6/recent/ticker-posts

NDLEA Ta Kama Tarin Gurbataccen Gas Mai Saka Mutane Dariya An shigo Da Shi Nijeriya

 


Kwanaki biyu bayan hukumar hana sha da da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta yi umarnin saka ido kan yaduwa nau’in gas na “lauhing gas”, mai kashe laka da saka dariya,


Hukumar NDLEA ta sanar da kama tarin sindarin Gas na “lauhing gas” a garuruwa biyu na kasar a ranar Juma’a.


Alfijir Labarai ta rawaito a ranar Talatar da ta gabata ne shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya, ya ba da umarnin saka kafar wando daya da masu safarar gas din.


Hukumar ta ce ana samun masu amfani da sinadarin na nitrous oxide, wanda aka fi sani da “laughing gas” domin jin dadi da sa maye.


Shugaban ya umarci duka ofisoshin hukumar a fadin Nijeriya da su fara daukar mataki kan masu sayar da gas din da masu amfani da shi ba bisa ka’ida ba.


A ranar Juma’a ne hukumar ta sanar da kama tarin sinadarin wanda ya kai kilgiram 64,863.5 a tashar bakin teku ta Apapa a Jihar Lagas da ke kudu maso yammaci, da kuma jihar Imo ta kudu maso gabashin kasar.


Hukumar ta ce kamen da ta yi ya biyo bayen tsegunta wa jami’anta a Apapa, game da shigo da sinadarin a ranar Laraba 12 ga watan nan na Yuli.