Wani miji da matarsa sun faɗa komar 'yan sandan jihar Yobe bayan tafkawa wani limami sata Ma'auratan sun yi basajar cewa suna so su karɓi Musulunci ne, inda daga bisa ni suka aikata ta'asar Sun yi awon gaba da babur ɗin ɗaya daga cikin 'ya'yan limamin da suka sauka a wurinsa
Sun je wajen liman da zummar suna so su karɓi Musulunci Kakakin ya ce Ibrahim mai shekaru 21 da Khadija mai shekaru 20, a ranar 4 ga watan Yuni sun je, wajen malamin da zummar cewa suna so su Musulunta.
Ya ƙara da cewa sun gabatar da kansu a matsayin Jude Emmanuel, ɗan ƙabilar Birom daga Farar-Kasa a Barkin Ladin jihar Filato da matarsa, da ta bayyana sunanta da Peace Sunday. Kakakin ya bayyana cewa bayan musuluntar da su ne, sai aka ce su zauna wajen babban Limamin Fika domin koyar da su ilimin addini da sauran abubuwa. Abdullahi ya ɗauke babur a gidan limamin da suke zaune wurinsa Dungus ya kuma ƙara da cewa bayan kwana ɗaya ne Abdullahi ya sanar da limamin cewa yana so ya samu toka daga wurin da tsawa ta faɗa don ya haɗa wani magani. A kalamansa ya ci gaba da
