Ticker

6/recent/ticker-posts

KE DUNIYA: Hukumar Hisba Ta Samu Nasarar Kama Matasan Da Ake Zargi Da Aurén Jinsí A Kano.


 KE DUNIYA: Hukumar Hisba Ta Samu Nasarar Kama Matasan Da Ake Zargi Da Aurén Jinsí A Kano.

Hisba ta yankewa matasan da suka auri junansu Abubakar da Khalifa hukunci bulala 1,000 kowannensu

Hukumar Hisba a jihar Kano ƙarƙashin jagorancin shugabanta Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta sami nasarar damƙe samari biyu da aka zarga da ƙoƙarin kulla auren jinsí.

A cikin wani bidiyo da ke yawo an ga samarin biyu masu suna Halifa da Abubakar suna ƙoƙarin sumbatár juna a yayin wani shagali wanda a ke zargin bikin baikon aurensu ne wato ‘Engagement

Sai dai matasan sun musanta zargin cewa bikin na baikon aurensu ne a yayin da Hisba ke tattaunawa da su.

A cewar Halifa, ya shirya bikin ne domin ranar zagayowar haihuwarsa wanda abokinsa Abubakar ya ba shi cake a baki shi ne ya kai bakinsa don ya gutsiri ragowar cake din da ke bakin Halifa.

Tuni Shugaban hukumar ta Hisba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayar da umarnin ci gaba da tsare matasan tare da faɗaɗa bincike domin gano gaskiya.

Hukumar Hisba ta sha alwashin ɗaukar tsattsauran mataki bayan samun matasan da laifin da a ke zarginsu da shi, da waɗanda suka halarci bikin da ma ɗakin taron ‘hall’ da aka yi bikin a cikinsa da duk mai hannu cikin bikin don ya zama darasi ga ƴan baya.