Wata matashiya mai suna Faiza Usman ta fitar da faifan Bidiyo wanda a ciki take roƙon gwamnatin Najeriya tasa doka mai tsanani ga samari inda ta ce
"Ina kira ga gwamnati duk namijin da ya isa yin aure kuma yaƙi yi a kama shi ya kai shi gidan yari na shekara 10 ko kuma ya biya tarar Naira Miliyan 10, sannan duk mijin da ya auri macce ya sake ta ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba to ya raba dukiyar sa biyu ya bata rabi" In ji ta kamar yadda ta bayyana a faifan Bidiyon