Ticker

6/recent/ticker-posts

Halin da ake ciki a kasar Niger a yanzu haka.

 


Halin da ake ciki a kasar Niger a yanzu haka.


Har yanzu shugaban kasa Bazoum yana hannun sojojin da ke kokarin yin juyin mulki a kasar, kuma fadar shugaban kasar na cigaba da tafiyar da shafukan ta na sada zumunta.


Har zuwa yanzu babu wata sanarwar da ta bayyana cikakken halin da ake ciki a fadin kasar baki daya. 


Abubuwa guda biyu ne kawai aka tabbatar, na farko shine jaridar "Air-Info Agadez" ta ruwaito cewa har zuwa yanzu shugaban kasar Bazoum bai sanya hannu kan takaddar ajiye mulki ba. 


Na biyu shine shugaban ECOWAS Bola Tinubu, ya turo tawagar jami'an tsaro na musamman da kuma shugaban jamhuriyar Benin Patrice Talon, da wasu tawagar tsoffin Gwamnonin Najeriya sun isa Yamai domin fara tattaunawa da sojin kasar Niger da suke tsare da Bazoum. 


Wasu gidajen Rediyo da talabijin na kasar suna cigaba da gudanar da shirye-shiryen su kamar yadda suka saba. 


Har zuwa yanzu sojojin da ke cigaba da tsare Bazoum basu ce uffan ba, bayan sunce za su gudanar da jawabi yau da misalin karfe 8 na dare. 


Abunda ya kamata mu cigaba da yiwa mutanen Niger shine, mu cigaba da musu Addu'a, Allah ya kare su daga makircin da ake kokarin kulla musu. Wata kila zuwa cikin dare ko zuwa da safe su bayyana halin da ake ciki a kasar. 


✍️ Comr Abba Sani Pantami